Lagos: An sace wani mataimakin shugaban makaranta da dalibai

Asalin hoton, Getty Images
Sace-sacen mutane ya zama ruwan-dare a Najeriya
Wasu 'yan bindiga sun sace wani mataimakin shugaban makarantar Model college da wasu dalibai hudu da ke Igbonla a yankin Epe a jihar Lagos.
Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Fatai Owoseni ya tabbatar da fkuwar lamarin a lokacin da yake yi wata ganarwa da manema labarai.
Mista Owoseni ya ce an gano biyu daga cikin daliban da aka sace.
" Mun samu wani mummunar labari da ke cewa an sace dalibai hudu da mataimakin shugaban makarantar Model, da ke Epe a safiyar ranar Alhamis.
Ya ce "wadanda suka sace su sun tafi da su a cikin jirgin ruwa. Muna jin labarin muka aike da jami'ai wurin. Mun gano dalibai biyu'.
Mista Owoseni ya kara da cewa har yanzu mataimakin shugaban makarantar da dalibai biyu suna hannun wadanda suka sace su.
'Jami'anmu sun fara nemansu. Muna hada kai dan sojojin ruwa domin nemo su a cikin ruwa dama duk inda suke', kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya rawaito.
Matsalar sace-sacen jama'a na kara karuwa a sassan Najeriya daban-daban.
Ko a farkon makon nan an sace tsohuwar Ministar Muhalli ta kasar Lauracier Malam da mijinta a hanyar Kaduna zuwa Abuja, kafin daga bisani aka sako ta.