Trump ya nemi gafara kan kalaman batsa

Trump

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Trump ya ce shi ba salihi ba ne

Dan takarar shugaban kasar Amurka na jam'iyyar Republican Donald Trump ya nemi gafara bayan wani bidiyo da aka fitar ya nuna shi yana yin batsa.

Bidiyon, wanda aka nada a shekarar 2005, ya nuna Mista Trump yana cewa "mata za su bar mutum ya yi musu komai idan mutumin ya shahara", yana mai cewa ya taba yunkurin sumbatar wata matar aure.

Wadannan kalamai dai sun jawo ce-ce-kuce, inda babbar abokiyar hamayyarsa ta jam'iyyar Democrat ta ce bai kamata mai yin irin wadannan kalamai ya zama shugaban Amurka ba.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar, Mista Trump ya nemi afuwa, yana mai cewa "kalaman ba sa nuna irin halina na hakika. Amma dai ina neman afuwa".

Ya kara da cewa, "Ban taba cewa ni salihi ba ne ko kuma ina rabe-rabe. Amma a kullum ina kokarin gyara halayena marasa kyau."