Nigeria: An haramta kungiyar 'yan uwa Musulmi a Kaduna

Asalin hoton, AP
Ana tsare da Sheikh Ibraheem Zakzaky tun watan Disamba
Gwamnatin jihar Kaduna a Nigeria ta haramta dukkan aikace-aikacen kungiyar 'yan uwa Musulmi ta 'yan Shi'a mabiya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.
Mai magana da yawun gwamna Nasiru El-Rufa'i, ya ce za a daure duk wanda aka samu yana aiki a matsayin dan kungiyar, tsawon shekaru bakwai a gidan yari.
Samuel Aruwan ya ce gwamnati ta dauki matakin ne, ta yin amfani da karfin da tsarin mulki ya bata, domin tabbatar da tsaro, da bin doka da oda, da zaman lafiya a jihar.
Kawo yanzu kungiyar, wacce ta sha yin fito-na-fito da hukumomi a baya, ba ta ce komai ba game da sanarwar.
Daruruwan mutane ne suka mutu lokacin da aka yi arangama a watan Disamba tsakanin 'yan kungiyar da sojojin Najeriya bayan sojin sun yi zargin cewa 'yan Shi'a sun yi yunkurin halaka shugabansu, Laftanar Janar Yusuf Buratai.
Sai dai 'yan kungiyar sun musanta zargin, suna masu cewa sojoji sun kashe dubban mabiyansu.
Hukumomi na tsare da Shugaban kungiyar Sheikh Ibraheem Zakzaky tun watan Disamba.
Dalilan haramta kungiyar
Asalin hoton, AFP
Mabiya Shia ba su da yawa a Nigeria
- Kwamitin binciken rikicin da aka yi a Zaria a watan Disamba ya gano cewa kungiyar ba ta da rajista
- Wani bangare na kungiyar Shi'a na dauke da makamai
- 'Yan kungiyar ba sa martaba dokar kasa
- Kuma ba sa mutunta hukumomi
- Tun bayan rikicin na Zaria kungiyar bata daina taron muzahara ba
- Kungiyar na mamaye makarantu da rufe hanyoyi ba tare da la'akari da hakkin jama'a ba
Kungiyar na da mabiya a sassan Najeriya da dama, amma wannan mataki zai yi aiki ne a jihar Kaduna kawai, inda nan ne hedikwatar ta 'yan Shi'a a kasar take.
Gwamnatin ta ce wannan mataki, wanda ya fara aiki a ranar Juma'a, ba a dauke shi ba ne domin hana mutane gudanar da addininsu kamar yadda dokar kasa ta basu dama.
Sai dai ta ce wannan dama tana da iyaka ta yadda ba za a amince ta tauye wa wasu hakkinsu ba.