'Yan shi'a sun mayar da martani kan haramta kungiyar

'Yan Shi'a a Nigeria

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Ana tsare da Sheikh Ibraheem Zakzaky tun watan Disamba

Kungiyar 'yan uwa musulmi a Nigeria ta maida martani kan harmata kungiyar da gwamunatin jihar Kaduna ta yi.

Kungiyar ta 'yan Shi'a ta ce haramcin da kaka yi mata ya saba ka'ida.

Mai magana da yawun kungiyar Malam Ibrahim Musa ya ce za za su kaluabalanci wannan mataki na gwamnatin ta Kaduna.

"Muna Allah wadai da wannan matakin da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka, ba mu yarda da shi ba, za mu kalubalance shi ta dukkan hanyar da ta dace inshaallahu." inji Ibrahim Musa.

Amma ya ce matakin bai basu mamaki ba, ganin irin take-taken hukumomin na Najeriya dangane da kungiyar.

Kakakin na 'yan shi'a yace duk abin da su ke yi bai saba dokokin Najeriaya ba.

A wata sanarwa da ta fitar ne dai ranar Juma'a gwamnatin ta jahar Kaduna ta ce ta soke wannan kungiya, haka kuma ta haramta dukkan ayyukan ta a dukkan fadin jahar.

Mai magana da yawun gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufa'i, ya ce za a daure duk wanda aka samu yana aiki a matsayin dan kungiyar, tsawon shekaru bakwai a gidan yari.

Samuel Aruwan ya ce gwamnati ta dauki matakin ne, ta yin amfani da karfin da tsarin mulki ya bata, domin tabbatar da tsaro, da bin doka da oda, da zaman lafiya a jihar.

Daruruwan mutane ne suka mutu lokacin da aka yi arangama a watan Disamba tsakanin 'yan kungiyar da sojojin Najeriya bayan sojin sun yi zargin cewa 'yan Shi'a sun yi yunkurin halaka shugabansu, Laftanar Janar Yusuf Buratai.

Sai dai 'yan kungiyar sun musanta zargin, suna masu cewa sojoji sun kashe dubban mabiyansu.

Hukumomi na tsare da Shugaban kungiyar Sheikh Ibraheem Zakzaky tun watan Disamba.

Dalilan haramta kungiyar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mabiya Shia ba su da yawa a Nigeria

  • Kwamitin binciken rikicin da aka yi a Zaria a watan Disamba ya gano cewa kungiyar ba ta da rajista
  • Wani bangare na kungiyar Shi'a na dauke da makamai
  • 'Yan kungiyar ba sa martaba dokar kasa
  • Kuma ba sa mutunta hukumomi
  • Tun bayan rikicin na Zaria kungiyar bata daina taron muzahara ba
  • Kungiyar na mamaye makarantu da rufe hanyoyi ba tare da la'akari da hakkin jama'a ba

Kungiyar na da mabiya a sassan Najeriya da dama, amma wannan mataki zai yi aiki ne a jihar Kaduna kawai, inda nan ne hedikwatar ta 'yan Shi'a a kasar take.

Gwamnatin ta ce wannan mataki, wanda ya fara aiki a ranar Juma'a, ba a dauke shi ba ne domin hana mutane gudanar da addininsu kamar yadda dokar kasa ta basu dama.

Sai dai ta ce wannan dama tana da iyaka ta yadda ba za a amince ta tauye wa wasu hakkinsu ba.