Ryan Giggs ya tattauna da Swansea City

Ryan Giggs ya ce aniyarsa ta sha bamban da na Swansea

Ryan Giggs ya ce aniyarsa ta sha bamban da na Swansea

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Ryan Giggs ya ce aniyarsa ta sha bamban da na Swansea

Ryan Giggs ya tabbatar da labarin da ke cewa ya tattauna da mutanen da suka mallaki Swansea City domin zama kocin kungiyar gabanin a bai wa Bob Bradley matsayin inda ya maye gurbin Francesco Guidolin.

Bradley ya kasance dan Amurka na farko da ya zama kocin kulob din da ke buga gasar Premier ta Ingila, inda aka nada shi a matsayin kocin Swansea ranar uku ga watan Oktoba.

Fitaccen dan wasan na Manchester United da Wales, Giggs, ya gana da masu kungiyar ta Swansea, sai dai ya ce manufofinsu ba su zo daya ba.

Ya shaida wa ITV Sport cewa, "Ina jin dadin tafiye-tafiye sai kawai mamallakan Swansea suka kira ni, kuma mun gana a lokuta da dama."

A cewar Giggs sun tattauna kan batutuwa da dama game da kwallon kafa da kuma mallakar kungiyar, amma daga baya ya gane cewa tasu ba za ta zo daya.

Tsohon dan wasan na dan wasan na Manchester United, mai shekara 42, ya zama kocin riko na kungiyar sannan daga bisani ya zama mataimakin koci karkashin Louis van Gaal kafin ya kama gabansa bayan Jose Mourinho ya zama koci.

Swansea City dai ita ce ta 17 a tebirin Premier kuma bata ci wasa ko daya ba tun da aka fara kakar wasa ta bana.