'Bongo ya karbi mulki da karfin tuwo'

Jean Ping ya nemi da a sanya wa Ali Bongo takunkumi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Kotun Tsarin Mulkin Gabon dai ta bayyana Ali Bongo a matsayin mutumin da ya lashe zaben kasar na watan Agusta.

Shugaban masu hamayya na kasar Gabon, Jean Ping, ya yi kira da a bujire wa shugaban kasar, Ali Bongo.

An dai bayyana Ali Bongo da mutumin da ya lashe zaben kasar na watan Agusta.

To amma mista Ping ya dage cewa shi ne ya ci zaben.

Masu sanya ido kan zabe na Tarayyar Turai, sun ce an samu wasu 'yan matsaloli musamman a garin su Mista Bongo.

An ce dai mutanen garin su Ali Bongo sun yi tsabe dari bisa dari.

Yanzu haka, Jean Ping yana kiran da a saka wa Ali Bongo da wasu makarrabansa takunkumi bisa abin da ya bayyana karbe mulki ta karfin soja.

Masu hamayya dai sun ce mutane da dama sun mutu sakamakon rikicin bayan zabe a kasar.