Matakin kawar da shan kwaya lokacin wasanni

Kwamitin IOC ya ce yana son kawo karshen matsalar

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Ana yawan samun 'yan wasa da suke shan kwayoyi masu kara kuzari a lokacin wasa

Kwamitin gasar Olympic ta Duniya wato IOC, ya yi kira da a fito da wani sabon tsarin da zai kawo karshen shan kwayoyi masu kara kuzari a lokacin wasanni.

Kwamitin wanda ya yi kiran a lokacin wani taron koli da aka gudanar a Switzerland, ya ce yana son ganin an bujiro da kwararan matakai da za su kawo karshen matsalar, ba kuma tare da nuna banbanci ba.

A karkashin sabbin tsare-tsaren, za a kafa wata sabuwar hukuma wadda za ta rinka yi wa 'yan wasa gwajin shan kwaya mai kara kuzari.

Sabuwar hukumar za ta kasance karkashin Babbar Hukuma mai yaki da shan kwaya a lokacin wasann ta Duniya wato WADA.

An dade dai ana zaman doya da manja tsakanin Kwamitin Wasannin Olympic na Duniyar da Hukumar Sanya ido kan shan kwayoyi a lokacin wasanni sakamakon rashin amincewa da haramta wa Rasha fafatawa a gasar Rio de Janeiro.