Wani matashi na son kai hari Jamus

Ana zargin Jaber Alkabr dan kasar Syria da kitsa hare-haren ta'addanci
Bayanan hoto,

'Yan sandan na Jamus ba su sami kowa ba a inda suka kai samame

'Yan sanda a jihar Saxony ta kasar Jamus sun kaddamar da wani samame da manufar farautar wani mutum dan kasar Syria bisa zargin kitsa harin bam.

Mai magana da yawun 'yan sanda ya ce sun kai samame kan wani gida da ke birnin Chemnitz a gabashin kasar.

'Yan sandan dai sun ce sun samu bayanan sirri ne daga Hukumar Leken Asiri ta kasar.

An dai bayyana mutumin da ake nema da suna Jaber Albakr, mai shekara 22.

Sai dai kuma jami'an tsaron sun ce ba su sami Jaber ba a gidan da aka kai samame amma kuma an sami wasu ababan fashewa.

Yanzu dai an killace wurin da aka kai samamen, a inda aka umarci mutane da su zauna a cikin gidajensu.