'Majalisa ba ta gayyaci Buhari kan tabarbarewar tattalin arziki ba'

Majalisar Dokokin Nigeria
Bayanan hoto,

Bakin 'yan majalisun ya zo daya wajen bukatar zuwan Shugaban don ya yi musu bayani

Fadar shugaban Nigeria ta ce babu wata takardar gayyata da majalisun dokokin kasar suka aika wa shugaba Buhari domin tattauna halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Mai taimaka wa shugaba Buhari kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa su ma a kafafen yada labarai kawai su ke jin wannan batu.

Wasu rahotanni na cewa 'yan majalisar sun gayyaci shugaban kasar ne domin ya musu bayani a kan halin matsin tattalin arzikin da Najeriyar ta samu kanta, da kuma kokarin da yake yi wajen fidda ita.

Bakin 'yan majalisar daga dukkan bangarorin jam'iyya mai mulki APC da ta 'yan hamayya, PDP ya zo daya kan gayyatar.

Suna bukatar sanin matakan da bangaren zartarwar ke dauka domin farfado da tattalin arzikin Najeriya da ya fada mawuyacin hali.

Cikin batutuwan da 'yan majalisar ke bukatar karin bayani shi ne batun rashin aikin yi da matasan kasar ke ciki.

Najeriya dai na fama da karayar arziki, sakamakon faduwar farashin mai a duniya, wanda shi ne abin da ta fi dogaro da shi wajen samun kudade.