Kaduna: An gano yarinyar da ta bata wata 7 baya

Mallam Nasir el-Rufa'i
Bayanan hoto,

Hukumomi a jihar sun ce suna gudanar da karin bincike kan lamarin

A jihar Kaduna da ke arewacin Nigeria an samu wata yarinya 'yar kimanin shekara biyar, watanni bakwai bayan da iyayenta suka bayyana bacewarta.

Tun a watan Maris da ya wuce ne a ka yi ta cigiyar yarinyar mai suna Sultana, wadda labarin bacewarta ya mamaye shafukan sada zumunta da muhawara na intanet na Facebook, da Twitter da Whatsup, da sauransu.

A lokacin iyayen yarinyar sun ce ta bata ne a yayin da ta fita domin zuwa makarantar Islamiyya.

Dambarwa dai ta barke tsakanin iyayen wannan yarinya da kuma wadanda aka gan ta tare da su, inda kowannensu ke cewa 'yarsa ce.

Yanzu dai rundunar 'yan sanda ta jihar Kaduna ta ce tana gudanar da bincike kan lamarin amma kuma ta ce tana zargin mutumin da aka gano yarinyar a wurinsa da laifin safarar mutane.