Trump ya rasa goyon bayan manyan jam'iyyarsa

Donald Trump ya rasa goyon bayan wasu jiga-jigan jam'iyyarsa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bidiyon kalaman batsar da Donald Trump ya yi ya kara jefa shi tsaka-mai-wuya

Manyan jiga-jigan jam'iyyar Republican sun janye goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasar Amurka a jam'iyyar Donald Trump, bayan bayyanar hoton bidiyon da ya yi kalaman batsa kan mata.

Cikin wadanda suka janye goyon bayan nasu akwai tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice, da tsohon dan takarar shugaban kasa Sanata John McCain.

Sai dai a nasa bangaren Mista Trump, ya sha alwashin ba zai janye daga takarar ba, kuma ba zai kunyata magoya bayansa ba.

Mista Trump dai ya shiga tsaka mai wuya ne, bayan bayyanar wani hoton bidiyo da ya yi kalaman batsa a shekarar 2005.