Kama alkalai: An dauko hanyar kashe dimukradiya— PDP

PDP
Bayanan hoto,

Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya

Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce dirar mikiya da jami'an hukumar tsaro ta farin kaya-DSS a kasar ke yi kan manyan alkalan kasar, an dauko hanyar kashe dimukradiyyar kasar ce.

Cikin wata sanarwa da Sakataren yada labaranta na kasa, Prince Dayo Adeyeye ya fitar, jam'iyyar ta yi zargin cewa dirar mikiyar, ta kara fito wa fili da salon kama-karya da gwamnatin Muhammadu Buhari ke yi.

Jam'iyyar ta ce a halin yanzu, alkalai hudu ne, da suka hada da Sylvanus Ngwuta da Inyang Okoro na kotun koli, da kuma Muazu Pindiga da Adeniyi Ademolada na manyan kotu na ke tsare a hannun hukumar ta DSS.

Jam'iyyar ta PDP ta ce da badan jajircewar da gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya yi ba, da jami'an hukumar ta DSS sun kama alkali na biyar, Mai shara'a Abdullahi Liman.

A cikin sanarwar, jam'iyyar ta PDP ta yi zargin cewa lokacin samamen, jami'an hukumar ta DSS sun ci zarafin alkalan, sannan suka lakadawa wasu ma'aikatan gidajensu duka.

Bayanan hoto,

Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya

Ta kuma bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na shugaba Muhammadu Buhari na mayar da bangaren shari'a 'dan amshin Shata'.

Ta ce kamata yayi a bi hanyoyin da ya kamata idan ana zargin alkalan da aikata laifi, ta hanyar aikewa ta takardun koke ga hukumar dake kula da ayyukan alkalai ta kasa.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Jam'iyyar PDP ta kuma bayyana wasu abubuwa da ta ce yi wa dokar Najeriya karan tsaye ne da gwamnatin Muhammadu Buhari ke yi, wadanda suka hada da yin dirar mikiya da jami'an DSS suka yi a majalisun dokokin jihohin Akwa Ibom da Zamfara, da ci gaba da tsare mutane da dama duk da umurnin sakinsu da kotu ta bayar.

"Ko a lokacin mukin kama-karya na Sani Abacha ba ayi wa ma'aikatan bangaren shari'a irin wannan dirar mikiya ba" PDP ta ce.

"Shugaba Buhari ya nuna ba ya mutunta turakun demukradiyar kasar nan. Ya nuna ya na so ya kashe dimukradiyyar, ya mayar da ita mulkin kama-karya", jam'iyyar ta kara da cewa.

Jam'iyyar ta ce gwamnatin Najeriyar ta ki ta mutunta umurnin kotun ECOWAS game da Kanar Sambo Dssuki.

PDP ta ce ya zama wajibi 'yan Najeriya su yi magana don kare mulkin demukradiya daga lalacewa.

A safiyar Asabar ne hukumar ta DSS ta ce ta gano makudan kudade a gidajen alkalan da ta kama.

Jami'an hukumar sun kaddamar da sumamen ne a babban birnin kasar, Abuja da Port Harcourt da Gombe da Kano da Enugu da kuma Sokoto.

Kuɗaɗen da aka samu a gidajen alkalai

  • N93,558,000.00
  • $530,087
  • £25,970
  • €5,680

Karin Bayani

An dade dai ana zargin alkalan Najeriya da cin hanci.

Ko makonni kimanin biyu da suka gabata sai da Hukumar da ke sa ido kan harkokin shari'a a kasar ta kori wasu manyan alkalai bisa samun su da laifin cin hanci.

An dai kori babban alkakin kotun jihar Kano, mai shari'a Kabiru Auta da babban alkalin kotun daukaka kara da ke zama a Ilorin, mai shari'a Mohammed Ladan Tsamiya.

Da kuma babban alkalin kotun Enugu, mai shari'a I. A. Umezulike.

Hukumar ta ce ta kori wasu daga cikin alkalan bisa karbar na-goro game da batutuwan da suka shafi zaben kasar na shekarar 2015.

Tun dai hawan mulkin kasar, Muhammadu Buhari, ya lashi takobin yaki da rashawa da cin hanci da suka yi wa kasar dabaibayi.