Shugabar gwamnatin Jamus na ziyara a Nijar

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A yayin ziyarar Angela Merkel za ta tattauna da Shugaba Mahamadou Issoufou

A jamhuriyar Nijar yau ne shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ke kai wata ziyarar aiki ta yini daya a kasar.

Markel za ta gana da shugaba Mahamadu Isufu kan batutuwan da suka hada da huldar da ke tsakanin kasashen biyu, da batun matsalar tsaro da bakin haure.

Za kuma su tattauna kan harkokin kiwon lafiya da ilimin kananan yara da tsaron kan iyaka musamman domin maganin kwararar bakin haure zuwa Turai.

Karamar ministar harkokin wajen Nijar Madame Elback Zainabu Tari Bako ta gaya wa BBC cewa shugabannin biyu za su yi nazarin yadda dangantaka tsakanin kasashen biyu tun ta shekara kusan 55 ta kasance.