Buhari ya kare DSS kan kama alkalai

Shugaba Muhammadu Buhari
Bayanan hoto,

Shugaba Buhari ya ce matakin na daga yakin da gwamnatinsa ke yi da almundahana

Fadar Shugaban Nigeria kare kanta kan matakin da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta dauka na kama wasu alkalai da cewa yaki ne da cin hanci da rashawa amma ba yaki da bangaren shari'a ba.

Mataimakin shugaban kasar na musamman kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, shi ne ya yi bayanin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Kakakin ya ce Shugaba Buhari yana martaba sashen shari'a a matsayin bangare na uku na gwamnati, a don haka ba zai taba yin wani abu da zai keta haddin 'yancin sashen ba.

Sanarwar ta kara da cewa Shugaba Buhari cikakken mai bin tafarkin dumokradiyya ne a baki da kuma aikace, kuma ba zai yi wani abu da zai saba wa kundin tsarin mulkin kasar ba.

Malam Garba Shehu ya nuna damuwa kan yadda wasu kafofin yada labarai ke gabatar da lamarin a matsayin sa-in-sa tsakanin sashen zartarwa da na shari'a yana mai cewa hakan bai dace ba.

Ya ce fadar shugaban kasar ta samu tabbaci daga hukumar tsaron ta DSS cewa ta bi duk matakan ka'ida, kmara samun takardar 'yancin bincike da kamawa kafin ta yi wa alkalan dirar mikiya.