Samsung ya bar kera Galaxy Note 7

Samsung Galaxy Note Seven

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yadda wata wayar Samsung Galaxy Note Seven ta kone kenan

Rahotanni daga Koriya ta Kudu na cewa fitaccen kamfanin kayan laturoni na Samsung ya sanar da dakatar da kera sabuwar wayarsa ta Galaxy Note Seven.

Samsung ya dauki matakin ne bayan samun rahotannin wayar na da matsala a batirinta har tana kamawa da wuta, alhalin sabuwar wayar an yi ta ne dan ta maye gurbin tsoffin wayoyin da kamfanin ya yi da su ma suke kamawa da wuta.

Tun ranar Juma'a da ta wuce kmfanin na Samsung bai ce uffan ba kan batun, wanda a baya ya ce ya na duba dalilin da ya sa wayar ta kama da wuta a Amurka.

Wakilin BBC a birnin Seoul ya ce wannan wani babban koma baya ne da kamfanin ya samu na dakatar da kera sabuwar wayar, saboda ana yi wa wayar ta Galaxy Note Seven, kallon wadda za ta yi gogayya da wayar iPhone Seven ta kamfanin Apple.