Ana binciken wasu iyaye a Indiya bayan yarsu ta mutu

Aradhana Samdariya

Asalin hoton, UMA SUD HIR

Bayanan hoto,

Mutuwar Aradhana ya jawo muhawara sosai a kafafen sada zumunta

'Yan sanda a India na binciken iyayen wata yarinya mai shekara 13 wadda ta mutu a makon da ya gabata bayan ta yi azumi na tsawon kwana 68.

'Yan Sandan da ke birnin kudancin Hyderabad sun shaidawa sashen Hindi na BBC cewa, suna so su sani ko an tirsasawa Aradhana Samdariya ta yi azumin ne.

Sai dai iyayenta sun dage kan cewa ita da kanta ta zabi ta yi azumin kamar yadda addinin Jainism, wanda daya ne daga cikin addini da ya dade a duniya, ya kayyade a yi.

Lamarin dai ya jawo muhawara a kan yin azumi a India.

Rahotanni na cewa Aradhana ta shafe kwana 68 tana shan ruwan zafi kawai. Kwana biyu bayan ta bar yin azumin, sai ta rasa ranta.

Masana sun yi ammanar mutum zai iya rayuwa ba tare da abinci ba na tsawon watanni biyu.

Wani mai magana da yawun 'yan sanda ya ce anyi karar iyayen bayan wata kungiyar kare hakkin yara sun yi korafi.

Azumin sa kai

Asalin hoton, KUMAR MANISH

Bayanan hoto,

Yarinya mai shekara 13 mai addinin Jain ta mutu sakamakon azumi 68

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"Za a tuhumi Laxmi Chand da Manshi Samdariya, iyayen Aradhana da sanadiyyar mutuwarta, saboda rashin kula da kuma yiwa yaro mugunta, " a cewar mai magana da yawun 'yan sandan.

Iyayen da ke zaune a Hyderabad, sun musanta cewa sun tursasawa 'yarsu yin azumi.

"Ta nemi mu bata izini ta yi azumin upvaas, azumin da ba a cin abinci kwata-kwata. Mun gaya mata ta bari bayan kwana 51 amma sai ta ki. Ita ta sa kanta yin azumin. Babu wanda ya ce dole sai ta yi." a cewar Mista Samdariya.

Sai dai masu fafutuka a dandalin a sada zumunta sun yi watsi da ikirarin iyayen.

"Ya kamata kasar Indiya ta ji kunyar cewa har yanzu ana irin wannan al'adar. Wani mai bai wa mahaifinta shawara ne ya ce idan ta yi azumi na tsawon kwanaki 68, kasuwancin babanta zai bunkasa." Dan fafutuka, Achyut Rao ya shaida wa sashen Hindi na BBC.

Ta kara da cewa, "An sa yarinyar ta dinga shan ruwa ne kawai daga fitowar rana har faduwarta. Babu gishiri ko lemun tsami ko wani abu a ciki."

Yin azumi mai yawan kwanaki ba wani sabon abu ba ne a tsakanin masu addinin Jains, wadanda 'yan tsiraru ne a Indiya.

Yin azumi ba sabon abu ba ne a wasu addinan - Musulumai ma suna yin azumi a watan Ramadan, haka kuma Kiristoci suna azumi lokacin Lent sannan Yahudawa basa cin abinci lokacin Yom Kippur, yayin da kuma mabiya addinin Hindu ke yin azumi a lokutan da ake bukukuwan addini.