Nigeria: Kama alkalai ya raba kan lauyoyi

Wasu lauyoyin Najeriya

Asalin hoton, EFCC

Bayanan hoto,

Batun kama alkalan na ci gaba da janyo cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya

A Najeriya kama alkalai bakwai da jami'an tsaro suka yi ya janyo bambanci ra'ayi a tsakanin lauyoyin kasar, inda wasu ke goyon baya wasu kuma na yin tur da kamen.

Fitaccen lauyan nan mai kare hakkin dan adam, Femi Falana ya goyi bayan kama alkalan, inda ya ce fannin shari'a a kasar ya dade yana fama da matsalar cin hanci da rashawa.

Sai dai a wata sanarwar da fitaccen lauyan ya fitar a Lagos, ya bukaci a gaggauta gurfanar da su a gaban kotu.

A daya bangaren kuma kungiyar lauyoyi ta kasa ta yi tur da kama alkalan da hukumar tsaro ta farin kaya ta yi.

Lamarin da ya sa ta kuma yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya sake su nan take ba tare da bata lokaci ba.

Haka kuma kungiyar ta kafa dokar ta baci a fannin shari'a saboda kamen ya shafi gudanar da shari'u.

A na ta bangaren kuwa, kungiyar ma'aikatan shari'a ta kasa JUSUN, nuna goyon baya ta yi ga matakin kama alkalan da gwamnati ta yi.

Shi ma wani babban lauya, Mike Ozekhome, ya shaida wa jaridar Premium Times cewa kamen barazana ne ga tafarkin demokuradiyya.

Amma jaridar The Guardian ta Nigeria ta ambato wani jigo a kungiyar ta JUSUN, Mista Okoi Obono Obla, yana shaida wa manema labaari a jihar Cross River cewa kamen bai sabawa doka ba, kuma wani ci gaba ne a yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Da alama dai wannan kame zai ci gaba da jan hankulan masu ruwa da tsaki a fagen shari'ar Najeriya tare da tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin lauyoyi.

Shi dai Shugaba Buhari ya dage cewa matakin wani bangare ne na yaki da cin hanci da rashawar da gwamnatinsa ta sa a gaba.