Ethiopia ta zargi Masar da Eritrea da kitsa tarzoma a kasarta

'Yan sandan kwantar da tarzomar a Ethiopia
Bayanan hoto,

Rikicin da ya kaure tsakanin 'yan kabilar Oromo da 'yan sandan Ethiopia ya yi sanadiyyar rasuwar mutum 55

Ministan sadarwan Habasha, ya ce wasu kungiyoyi a kasashen Eritrea da Masar na kara rura wutar rikicin da ya yi sanadiyyar kafa dokar ta-baci ta watanni shida da aka yi a kasar.

Getachew Reda, ya yi zargin cewa wasu daga kasashen waje ne ke bai wa kungiyoyin adawa tallafi na kudi ba da yawun gwamnatin kasar ba.

Dokar ta-bacin da aka kafa, za ta tabbatar da tura dakarun tsaro wajen dakile zanga-zangar.

Dokar ta biyo bayan mummunar zanga-zangar adawa da manyan kabilun kasar biyu suka shafe watanni suna yi.

Rikicin dai ya kara ruruwa ne a farkon wannan watan, inda akalla mutane 55 suka rasu a lokacin boren a yayin wani biki na kabilar Oromo.