Abin da DSS ta yi bai dace ba — Mahmud

Alkalin alkalai, Mahmud Mohammed ya ce za su tattauna ranar Talata kan matsalar
Alkalin alkalan Najeriya, mai shari'a Mahmud Mohammed, ya ce dirar mikiyar da jami'an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta DSS, suka yi, abin takaici ne kuma ya zo mu su da ba-zata.
Mai shari'a Mohammed ya bayyana rashin jin dadinsa kan al'amarin ne ranar Litinin, yayin wani taron ban-kwana ga alkalin Kotun Kolin Kasar, Suleiman Galadima wanda ya yi ritaya.
Alkalin alkalan ya ce samamen da jami'an DSS suka kai wa alkalan ranar Juma'a da Asabar, abin Alla-wadarai ne.
Sai dai kuma ya shaida cewa Hukumar da ke Kula da Harkokin Shari'a ta Kasar za ta zauna ranar Talata domin tattaunawa kan yadda za a tunkari al'amarin.
Mai shari'a Mahmud ya kuma goyi bayan matakin da Kungiyar Lauyoyi ta Dauka kan kamaun da aka yi wa alkalan.