Za mu tallafa wa Niger kan tsaro — Merkel

Nijer dai ta nemi da Jamus ta ba ta miliyan dubu na Euro domin tun karar matsalar bakin haure
Bayanan hoto,

Shugaban Jamhuriyar Niger, Mahamadou Issoufou ya cimma wasu yarjeniyoyi da shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Markel ta yi alkawarin taimaka wa Jamhuriyar Niger kan sha'anin tsaro da ilimi da aikin gona da kuma batun bakin haure.

Hakan dai ya tabbata ne yayin ziyarar aiki ta yini daya da ta kai kasar, ranar Litinin.

Markel dai ta gana da shugaba Mahamadu Isufu kan batutuwan da suka hada da huldar da ke tsakanin kasashen biyu da batun matsalar tsaro da kuma ta bakin haure.

Ministan Harkokin wajen Niger, Ibrahim Yakuba, ya ce kasar Jamus ta yi alkawarin tallafawa kasar da motoci da kayan sadarwa sannan kuma a ba su horo.

dangane kuma da batun bakin hauren da ke bi ta Nijer zuwa Turai, Jamus ta nemi Niger din da ta rinka dakatar da masu wucewar.

To sai dai kuma jamhuriyar ta Niger ta nemi da Jamus ta ba ta miliyan dubu na Euro amma dai Jamus din ba ta ce komai ba tukunna.

Angela Merkel dai ta kai irin wannan ziyara Mali ranar Lahadi kuma daga Niger din za ta wuce ne zuwa Ethiopia.