Ba zan kare Trump ba — Paul Ryan

Donald Trump ya nemi afuwa kan kalaman da ya yi

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Paul Ryan ya ce zai kare kujerun 'yan Majalisar Wakilai na jam'iyyar Republican amma ba zai kare Trump ba

Mutumin da ya fi kowa mukami a jam'iyyar Republican a Amurka, Paul Ryan, ya ce ba zai kare Donald Trump ba, bayan kalaman da ya yi kan mata sun jawo kace-nace.

Paul Ryan wanda kakakin majalisar Wakilan Amurka ne ya sha alwashin kare kujerun 'yan jam'iyyar tasa a majalisa.

Amma kuma bai nuna goyon bayansa ba ga dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar tasu, Donald Trump.

Daman dai abokiyar hamayyarsa, Hillary Clinton ta nuna rashin amince wa da tuban da Trump ya yi kan kalaman batsa da ya yi ga matan.

Mista Trump dai, a cikin wani faifan bidiyo da aka fitar ya ce mata za su iya kyale mutum ya yi duk abin da ya ga damar yi da su.