Syria: France na son ICC ta hukunta Russia

Rasha da Syria ba sa cikin kasashen da suka amince da kotun ICC

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Rasha ta hana Faransa da Spaniya rawar gaban hantsi a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban Faransa, Francois Hollande ya bayar da shawarar cewa ya kamata Rasha ta fuskanci hukuncin laifukan yaki kan rawar da take takawa a Syria.

Mista Hollande ya shaida wa gidan talbijin na kasar cewa hakan na nufin maka Rasha a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya wato ICC.

Ya kuma ce bai zama lallai ya amince ya yi ido da ido da shugaban Rasha, Vladimir Putin, ba, wanda zai ziyarci Faransa mako mai zuwa.

A makon da ya gabata ne dai Rashar ta danne yunkurin Faransa da Spaniya a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, kan kawo karshen rikicin Syria.

Rasha dai ta sha musanta sukar ta da ake yi wajen kai hare-hare kan fararen hula.

Ta ce tana kai hare-hare ne kan kungiyar 'yan ta'adda da ke Syria.

Rasha da Syria dai duka ba sa jerin kasashe da hukuncin kotun ICC zai iya tasiri a kansu.