Matakin korar Rahma Sadau ya yi tsauri — Ali Nuhu

Ya ce kamata ya yi a warware matsalar ba sa an fada kowa ya ji ba
Bayanan hoto,

Ali Nuhu ya ce hukuncin da aka yi wa Rahma Sadau ya yi dai-dai amma kuma ya yi tsauri

Fitaccen jarumin fina-finan Hausar nan, Ali Nuhu, ya ce hukuncin da Kungiyar Masu hada fina-finan Hausa, MOPPAN ta yi na korar Rahama Sadau, ya yi tsanani.

Ya ce kamata ya yi a dauki hukuncin da bai kai na kora ba kamar dakatar da 'yar wasan na dan wani lokaci.

Sai dai kuma Ali Nuhu wanda ya shaida hakan a wata hira da jaridar Daily Trust, ya ce 'yar wasan ta karya dokokin kungiyar.

Dangane kuma da mutanen da suka rinka yayata hotunan jarumin rungume da mata, a kafafen sada zumunta, Ali Nuhu ya ce, ya yi hotunan ne da dadewa tun kafin kungiyar MOPPAN ta haramta yin hakan.

A makon da ya gabata ne dai kungiyar ta MOPPAN ta sanar da korar Rahma Sadau daga harkar fina-finan Hausa saboda rungumar wani mawaki.