Gwamnatin Burundi ta kori jami'an MDD

Pierre Nkurunziza
Bayanan hoto,

Tun a shekrr da gabata ne Burundi ta fad rikicin siyasa

Kasar Burundi ta kori masu bincike uku na Majalisar Dinkin Duniya, bayan zargin da suka yi wa gwamnati da take hakkin bil'adam.

A wani rahoto da aka wallafa a watan da ya gabata, da masu bincike suka gabatar ya nuna cewa dubban 'yan kasar aka azabtar, wasu kuma an ci zarafin su ta hanyar lalata da su, da wadanda aka neme su sama ko kasa a ka rasa a lokacin rikicin siyasar da Burundin ta fada ciki.

Sun kuma yi gargadin aikata kisan kare kiyashi a kasar. Matakin da Burundi ta dauka na korar jami'an Majalisar Dinkin Duniya na zuwa ne kwanaki kadan da kasar ta sanar da shirin ficewa daga kotun hukunta manyan laifuka da ke Hague wato ICC.

Fiye da mutane dari biyar ne suka rasu, a tashin hankalin da ya barke a Brundi a shekarra da ta gabata,saboda matakin yin tazarce a karo na uku da shugaba Pierre Nkurunziza ya dauka.