Putin ya janye ziyara zuwa Faransa

Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya janye ziyara zuwa Faransa
Bayanan hoto,

Shugaban Faransa, Francoise Hollande ya nemi ICC ta hukunta Rasha

Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya soke ziyarar da ya shirya kai wa Faransa saboda sa-in-sa da suke yi a kan rikicin Syria.

Mista Putin dai na gab da saduwa da Francoise Hollande a wannan watan.

Amma kuma sakamakon maganar da gwamnatin Faransa ta yi cewa ziyarar ta dogara ne kacokan ga tattaunawa kan rikicin Syria, al'amarin da ya sa aka soke ziyarar.

A ranar Litinin ne dai shugaban Faransa, Francois Hollande ya bayar da shawarar cewa ya kamata Rasha ta fuskanci hukuncin laifukan yaki kan rawar da take takawa a Syria.

Ya kuma ce bai zama lallai ya amince ya yi ido da ido da shugaban Rasha, Vladimir Putin, ba, wanda zai ziyarci Faransa mako mai zuwa.

A makon da ya gabata ne dai Rashar ta danne yunkurin Faransa da Spaniya a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, kan kawo karshen rikicin Syria.