Ko nawa ginin layin dogo zai laƙume a Najeriya?

Shugaba Buhari ya ce za su kashe fiye da Dala biliyan biyu a gina titunan jirgin
Bayanan hoto,

Kamfanin General Electric ya ce zai zuba Dala biliyan biyu wajen gina layikan dogon

Kamfanoni daga kasashe daban-daban a duniya, sun fara zawarcin batun gina layukan dogo da Najeriya take son yi.

Yanzu haka, rukunin kamfanoni na General Electric da ke da Hedikwata a Amurka, ya bayyana aniyarsa ta gina tare da tafiyar da layikan dogo a Najeriya.

Rahotanni sun ce kamfanin ya tabbatar da cewa zai kashe sama da dala biliyan biyu wajen gina titunan.

Shugaban Najeriya dai Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen samar da layukan dogo a fadin kasar.

Sai dai kuma kasar na fuskantar karayar tattalin arziki.

Hakan ne kuma ya sa kasar gayyatar kamfanoni masu zaman kansu domin su gina da kuma tafiyar da titunan jirgin na kasa har zuwa wasu shekaru.

Sannan kuma daga bisani su mayar wa da gwamnati.

Daman dai Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani kamfanin kasar China wajen zamanantar da layikan dogon kasar a kan kudi dala biliyan 5.

A shekarar 1898 ne dai Turawan Mulkin Mallaka suka fara gina layukan dogo a fadin kasar.

A 2016 ne kuma shugaba Muhammadu Buhari ya kammala da bude layin dogon da gwamnatin Goodluck Jonathan, ta fara, daga Kaduna zuwa Abuja.