Facebook ya bude wani sabon dandali

Kamfanin sadarwa na Facebook

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kamfanin sadarwa na Facebook ya kafa wani dandali wanda zai bai wa 'yan kasuwa damar kafa nasu manhajojin.

Kamfanin sadarwa na Facebook ya bude wani sabon dandali, wanda zai bai wa wasu kamfanoni damar kafa tasu manhajar, domin kasuwanci.

Manhajar, wadda ke kama da ta Facebook, na dauke da na'urorin daukar bidiyo da tura sakwanni.

Sai dai kuma ba a hade suke wuri guda da sashen da ke nuna sunan mutum da wasu abubuwa na kashin kansa ba.

An tsara manhajar ne domin ta maye gurbin wasu manhajojin da ake amfani wajen kasuwanci kamar manhajar tura sakwannin email.

Wani mai sharhi dai ya ce wannan sabon dandali zai fuskanci kalubale daga sauran kamfanoni irinsa da suke gogayya da shi.

Za a sa manhajar a kasuwa domin gogayya da wasu manhajojin kamar Yammer ta Microsoft, masu hada-hadar kasuwanci ta hanyoyin sada zumunta.

Da kuma manhajar Slack, wadda ake amfani da ita wajen tura sakwanni.

Wani jami'i a Lewis Consultancy ya ce "Ba wai samar da hanyoyin kasuwanci ta sada zumunta ba ne kadai, zai ba su damar gogawa da wasu manhajojin kamar Google Cloud."

Ana dai amfani da Google Cloud ne wajen musaya da gyara bayanai.

Ya kuma kara da cewa, "Zai ratsa wurare da dama a matsayin abu muhimmi guda daya."