An zargin Ministan kudi da rashawa a Afrika Ta Kudu

Ministan Kudi na Afrika Ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An zargi Ministan kudi na Afrika Ta Kudu da cin hanci da rashawa.

An gabatarwa ministan kudi na Afirka ta Kudu, Pravin Gordhan, takardar bukatar sa ya bayyana a gaban kotu bisa zargin sa da rashawa.

Tuhumar da ake masa ta na da nasaba da zargin aikata ba dai-dai ba da ake mushi, lokacin da yake shugabantar hukumar karban kudin haraji ta kasar.

Mista Pravin ---wanda a yanzu baya jituwa da shugaba Jacob Zuma ---ya sha yin watsi da zarge-zargen, wadanda ya bayyana a matsyin bita-da-kullin siyasa.

Amma babban mai shigar da kara Shaun Abrahams, ya ce babu hannu gwamnatin kasar a cikin shari'ar.

A 'yan watannin da suka gabata, Afrika Ta Kudu ta sha da kyar wajen neman kaucewa faduwar darajar ta wajen karbar bashi zuwa rukunin da zai mayar da ita kamar tarkace, matsayin da Ministan kudin kasar ke ta fadi da tashin ganin bai faru ba.