MDD ta damu kan makomar Kongo

Joseph Kabila
Bayanan hoto,

Neman tazarce a karo na uku na Joseph Kabila ya jefa Dumokuradiyyar Kongo cikin rikici

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya samu gargadin cewa Jamhuriyar Dumokuradiyyar Kongo za ta sake fadawa cikin mummunan tashin hankali.

Wakili na musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Kongon Sambo Sidikou, ya ce cikin dan takaitaccen lokaci kasar za ta iya afkawa cikin tashin hankali.

Ya kara da cewa barazanar da dakarun wanzar da zaman lafiya nasa su 18000 ke fuskanta ta fi karfinsu matuka.

'Yan hamayya na ganin cewa yunkurin shugaba Joseph Kabila na yin tazarce a karo na uku ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar, wanda a ka'ida wa'adinsa na mulki a karo na biyu zai kare a watan Disamba mai zuwa.

Mutane da dama ne suka rasa ransu a rikicin kin jinin gwamnati da aka yi a Kinshasa a watan da ya gabata.