IS ta shiga tsaka-mai-wuya - Amurka

Mayakan IS
Bayanan hoto,

Wani daga cikin hotunan farfaganda na kungiyar IS

Wani sabon bincike da aka gudanar ya nuna cewa an samu gagarumar raguwa a yawan bidiyo da hotunan farfagandar da kungiyar da ke ikirararin kafa daular Islama, IS ke watsawa.

Kwalejin hafsoshin sojin Amurka wadda ta tattara bayanan ta ce lamarin ya nuna cewa asarar yankuna da kuma kashe manyan jami'an IS ya sha kan ayyukan kungiyar na farfaganda.

Ko a ranar Litinin kungiyar ta fito fili ta tabbatar da cewa tsohon babban jami'inta na farfaganda, Abu Muhammad al-Furqan, ya mutu a watan da ya gabata.

Kwararru a makaranta sun yi nazari a kan dubban hotuna da bidiyo da sanarwa da kungiyar ke fitarwa, inda suka ayyana cewa yawan wadannan abubuwa na yada manufa da ayyukan kungiyar sun ragu sosai.

Masanan sun ce abubuwan na farfaganda d tke fitarwa sun ragu daga 700 daga watan Agusta na 2015 zuwa kasa da 200 zuwa watan Agusta na 2016.