Dan Syria ya kashe kansa a kurkukun Jamus

Asalin hoton, DANIEL KARMANN
Wurin da aka kai harin bom a Jamus
Wani mutum dan kasar Syria da ake tuhuma da tsara kai wani harin bom a kasar Jamus ya kashe kansa.
An samu gawar Jaber Albakr a rataye a dakinsa na kurkuku a birnin Leipzig.
Wani dan uwansa dan kasar Syria ne dai ya damka shi ga 'yansanda bayan ya dauki kwanakki biyu a boye.
Lauyan da ke kare Jaber Albakr ya bayyana mutuwarsa a zaman wani abin kunya saboda inji shi ma'aikatan kurkukun na sane da cewar akwai yiwuwar ya kashe kansa.
'Yansanda sun ce sun samu daruruwan giram-giram na abubuwa masu fashewa a gidansa da ke birnin Chemnitz.