Sojan Myammar sun bindige musulman Rohigya 10

Macen kabilar Rohingya
Bayanan hoto,

Shekaru hudu ke nan ana tashin hankali a jihar

Kafafen watsa labaran kasar Myammar sun ce sojojin kasar sun kashe mutane goma a jihar Rakhine a rana ta hudu ta tashin hankalin da ya barke a kasar.

Majiyar gwamnati ta ce sojojin sun kutsa cikin kauyukkan musulmi 'yan kabilar Rohingya domin zakulo masu hannu a hare-haren da aka kai wa jami'an tsaron kasar inda suka kashe goma daga cikinsu a ranar Laraba.

Sai dai kuma a shafukan sada zumunta na Rohinjawa da kuma na masu fafutuka an nuna hotunan gawawwakin mutane cikin jini da suka ce na Rohinjawan mazauna kauyukka ne da basu ji ba su gani ba; wadanda sojojin suka karkashe a zaman ramuwar gayya ga harin da aka kai musu.

Jihar ta Rakhine dai a rabe take tsakanin mabiya addini Buddha da al'ummar ta Rohingya wadanda suka kwashe shekaru aru-aru suna zaune a yankin, amma gwamnati ta ki amincewa da su a zaman 'yan kasa.