'Yar Chibok ɗin da aka fara cetowa daha hannun 'yan Boko Haram

Asalin hoton, NIGERIAN ARMY
An samo Amina da jariri dan wata hudu.
A ranar Talata ne aka ceto wata yarinya daga dajin Sambisa, wani yanki da ke arewa maso gabashin Najeriya, fiye da shekara biyu bayan ƙungiyar Boko Haram ta sace ta daga makarantar sakandaren Chibok.
Yarinyar dai ita ce ta farko da aka ceto, cikin mata 219 da Boko Haram ɗin suka yi garkuwa da su.
Ga dai abubuwan da aka sani game da ita:
Ɗaya daga cikin shugabannin al'ummar Chibok, Hosea Abana Tsambido, ya shaida wa BBC cewa shekarar yarinyar 19, kuma ta fito ne daga Mbalala, wanda ya kai nisan kilomita 10 daga garin na Chibok.
Wani ɗan jarida Samson Aboku, wanda shi ma ya fito daga Mbalala , ya ce mutanen garin sun kai akalla 30,000 kuma yawancinsu mabiya addinin Kirista ne, amma ita Amina Musulma ce.
Mbalala: Garin da ya rasa 'ya'ya mata
Samson ya ƙara da cewa, yarinyar ta girma ne a wata 'yar bukka tare da mahaifiyarta.
Baban ta ya rasu, amma cikin 'ya'ya 13 da uwar ta haifa, su biyu kacal, watau da yarinyar da yayanta, suka rayu.
Aboku Gaji, wanda ke jagorantar wasu ƙato da goran da suka tsinto Amina ya bayyana wa BBC yadda haduwar ta da mahaifiyarta ta kasance.
Ya ce, "Lokacin da muka iso gidansu, mun tarar da ƙofa a rufe, sai na ce maman nata ta fito ga baƙuwa, tana ganin ta sai ta soma kiran sunan ta cike mamakin ganin ta.
Daga bisani sai suka rungume juna, har kamar za su fadi kasa, sai da muka rike su.
Yarinyar da sai ta soma bai wa uwarta baki, tana cewa 'Don Allah mama ki yi haƙuri, ki kwantar da hankalin ki, ban taba tsammanin zan sake ganin ki ba, ki share hawayen ki. Allah Ya bamu damar sake haduwa.'
Haka nan Amina ta ce wa mahaifiyarta."
Asalin hoton, NIGERIAN ARMY
An sami Amina Ali Nkeki tare da jaririyarta 'yar wata hudu, da kuma wani mutumi da ya ce shi ne mijinta.
Blamadu Lawan, shi ne mataimakin shugaban makarantar sakandaren Chibok, inda yarinyar take kafin a sace ta, ya kuma shaida wa BBC cewa, ɗaliba ce mai nutsuwa.
Lawan ya ga lokacin da aka wuce da ita cikin gari ranar Laraba, inda ya ce ya ga duk ta canza kamanni, ta rame.
A lokacin da ta ke hannun Boko Haram, yarinyar ta haifi 'yar ta mace, wacce ake iya gani a wani hoto da sojojin Najeriya suka dauka.
Ɗaya daga cikin masu fafutukar nan na #BringBackOurGirls, Hadiza Bala Usman, ta shaida wa BBC cewa watan jaririyar huɗu.
A wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar, ta ce an ceto yarinyar ne tare da wani mutumi mai suna Mohammed Hayatu, wanda ya ce shi ne mijinta, duk da cewa sojojin na zargin sa da zama ɗan kungiyar Boko Haram.