'Yan matan Chiɓok sun isa Abuja

Asalin hoton, BBOG
'Yan matan Chibok suna gana wa da mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo
'Yan matan Chibok guda 21 da kungiyar Boko Haram ta saki da safiyar Alhamis, sun sauka a Abuja, babban birnin kasar, da yammacin Alhamis din.
Mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ne ya karbi 'yan matan a fadar shugaban kasa.
Da farko dai sai da aka kai 'yan matan Kaduna domin a duba lafiyarsu.
An kuma tuntubi iyayensu kan sunayensu na hakika da ma tabbatar da cewa 'yan matan na garin Chibok din ne.
Wata majiyar soji wadanda suka yi aikin karbar 'yan matan Chibok din, ta ce hudu daga cikin 'yan matan sun zo da 'ya'ya.
Wasu rahotannin ma sun ce 18 daga cikin 21 ne suka haihu.
Da misalin karfe 5:30 na safiyar Alhamis din ne aka saki 'yan matan, a garin Banki da ke kan iyakar Nigeria da Kamaru.
Asalin hoton, Getty Images
Sama da shekara biyu kenan 'yan matan na hannun Boko Haram
Rahotanni kuma sun ce Kungiyar Agajin Gaggawa ta Kasa da Kasa wato Red Cross International da gwamnatin Switzerland ne suka wuce gaba wajen sakin 'yan matan.
Wasu rahotannin sun ce sai da gwamnatin kasar ta saki wasu kusoshin kungiyar Boko Haram guda hudu, kafin kungiyar ta yarda ta saki 'yan matan.
Amma gwamnatin kasar ta musanta hakan, a inda ta ce an saki 'yan matan ne sakamakon tattaunawa da ta fara da 'ya'yan kungiyar.
Wannan dai shi ne karon farko da aka saki 'yan matan na Chibok ta hanyar tattaunawa.
Sai dai kuma ba a fayyace ko da wane bangare na Boko Haram aka tattauna ba kasancewar a baya-bayan nan an samu wagegiyar baraka tsakanin 'yan kungiyar ta Boko Haram, wato bangaren Abubakar Shekau da na Albarnawi.
A watan Aprilun 2014 ne dai kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da 'yan matan sakandaren garin Chibok su fiye da 200.
Asalin hoton, Getty Images
Sace 'yan matan Chibok ya ja hankalin duniya sosai
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, Minti daya da BBC Safe 20/01/2021, Tsawon lokaci 1,14
Minti Ɗaya da BBC na Safiyar 20/01/2021 wanda Sani Aliyu da Nabeela Mukhtar Uba su ka karanto.