Nigeria: Hirar Aisha Buhari na shan yabo da suka

Aisha ta ce wadanda ba su da ko katin zabe ne suka fi cin moriya.
'Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyi da suka sha bamban da juna kan kalaman da uwar gidan shugaban kasar ta yi kan yadda mai gidan nata ke tafiyar da harkokin mulkin kasar mafi yawan jama'a a nahiyar Afrika.
Hajiya Aisha Buhari ta bai wa kusan dukkanin 'yan kasar mamaki da kalaman nata da ta yi a cikin wata kebantacciyar hira da BBC wadda aka fara watsawa ranar Jumu'a cewa mai gidanta ya yi watsi da mafi yawancin wadanda suka taimaka masa ya hau mulki.
''Wadanda ba su yi wahala ba; wadanda ko katin zabe ba su da shi su suka zauna a kan mutane suke yin komai da komai. Abin da nake guje musu (su manyan APC) shi ne boren da mutum miliyan 15 za su yi," in ji ta.
To sai dai a yayin da 'yan kasar da yawa ke ganin kalaman nata gaskiya ne, wasu na yi musu kallon wani katsalandan a cikin harkokin gudanar da gwamnati.
'' Mu wadanda muka zabi gwamnati Shugaba Muhammadu Buhari mun dade muna fadin akwai matsaloli cikin mulkinsa amma wasu na ganin ba haka ba ne, to yanzu kurunkus magana ta fito daga bakin da ba ya karya'' inji wani dan kasar mazaunin Kano.
Amma kuma wani dan Najeriyar cewa yake: '' wannan ya nuna min cewa shugaban kasa ba a yi masa dole, hatta matarsa ma ba ta isa ta saka a daki ba ta gaya masa abu ya yi dole ba. Lalle Muhammadu Buhari namiji ne ba wanda yake juya shi.''