Nigeria: Sojoji sun harbe dan kwallo Izu Joseph

Izu Joseph
Bayanan hoto,

Kawo yanzu rundunar sojin Najeriya bata ce komai ba game da lamarin

Mahaifin wani dan kwallon kafa a Najeriya, ya ce sojojin kasar da ke fada da masu tayar da kayar baya a yankin Naija Delta sun harbe dan wasan har lahira.

An harbe Izu Joseph, wanda dan wasan baya ne, a mahaifarsa da ke jihar Bayelsa mai arzikin man fetur.

Mahaifin Eze, ya ce sojojin hadin gwiwa ne suka harbe shi lokacin da suke neman masu tayar da kayar baya a yankin.

Wakilin BBC a fannin wasanni Oluwashina Okeleji, da ke Legas, ya ce sai bayan da aka kashe shi sannan aka gano cewa dan kwallo ne.

Kawo yanzu dai rundunar sojin Najeriya ba ta ce komai ba game da lamarin.