Masu kamun kifi mai kama da Kaguwa

Wata mace tana shiga cikin ruwan da ke wurin shakatawa ta na Bwejuu

Asalin hoton, Tommy Trenchard

Ruwan da ke dauke da sinadari mai kama da garin hoda na bakin ruwan gabashin Zanzibar wuri ne da masu yawon bude idanu suke zuwa shakatawa.

To amma a kowace rana, a dai-dai lokacin da igiyar ruwan take hankoro, kuma masu shakatawa suke komawa dakunan otal-otal dinsu, wasu tsirarun maza da mata suna shiga cikin ruwan dauke da sanduna da fatsa domin farautar kifin ruwa mai kama da kaguwa wato Octopus wanda ya fi kowanne dadi a Zanzibar.

Asalin hoton, Tommy Trenchard

A duk lokacin da igiyar ruwan ta kada, idan mai farauta ya gwanance to zai iya samun kifin mai kama da kaguwa kamar guda 10 wadanda suke rabe a tsakankanin duwatsun ruwa da ciyayin bakin ruwa.

Wannan kifin ne nama ga masu yawon bude ido da ke zaune a otal-otal din da ke wurin sannan kuma shi ne nama ga al'ummar da ke zaune a bakin ruwa.

Asalin hoton, Tommy Trenchard

Su wadannan kifaye da ke a cikin ciyayin da ke bakin ruwa sun zama hanyar neman abincin al'ummar yankunan.

Asalin hoton, Aurelie Marrier d'Unienville

Tanzaniya ce kasar da ta fi kowacce a yammacin kogin India, yawan kifaye nau'in Kaguwa.

Asalin hoton, Tommy Trenchard

Abdullah Ali, mai shekara 35, yana kimtsa kwale-kwalensa domin tafiya neman kifaye dangin Kaguwa daga kauyensa Dongwe.

Yanzu haka maza ne suka mamaye sana'ar kamun kifin duk kuwa da cewa asali sana'ar ta mata ce

Asalin hoton, Aurelie Marrier d'Unienville

"Sana'ar kamun kifin mai kama da Kaguwa ta taimaka min wajen tafiyar da rayuwata," in ji Ali, wanda yake samun £1.90 kwatankwacin $2.30 a kowane kilogiram na kifin.

Asalin hoton, Tommy Trenchard

Bisa kididdigar da Hukumar Kula da Abinci ta Duniya ta fitar, kifin mai kama da Kaguwa da ake kamawa a Tanzaniya ya kai tan 482 a 1990 zuwa fiye da tan 1,250 a 2012.

Asalin hoton, Tommy Trenchard

Ciyayin da ke hade da duwatsu a bakin ruwa sun zamo maboya ga kifayen kuma hakan ya sa masu neman kifin wadanda ba su kwarance ba, ba sa iya kama su.

Sannan kuma dubban ciyawar kainuwa da ke lullube kifayen wata matsalar ce ga masu yin su.

Asalin hoton, Tommy Trenchard

Mariam, wata mai yin sun kifin a kauyen Bwejuu, ta fada cikin ruwan domin yin linkaya bayan kammala aikin neman kifi da safe.

Asalin hoton, Tommy Trenchard

Mama Juma, wadda ta dade tana sun kifin, tana zagayawa a cikin ruwan da ana iya ganin kasansa da ke kusa da bakin ruwa na Paje domin gano wuraren da kifayen ke makale.

Asalin hoton, Aurelie Marrier d'Unienville

Wata mata tana neman kifi ita kadai da yammaci a wata gona da ke Bwejuu.

Mafiya yawan mazauna Bwejuu suna samun kudadensu ne daga sana'ar kifin mai kama da Kaguwa.

Asalin hoton, Tommy Trenchard

Gasasshen kifin mai kama da Kaguwa shi ne abincin da ake saya a kasuwa da daddare a garin Stone.

Mafi yawancin kifin da ake kamawa a Tanzaniya ana fitar da shi zuwa Turai ne to amma kuma kasuwar kifin tana matukar samun tagomashi daga masu yawon bude ido.

Tommy Trenchard da Aurelie Marrier d'Unienville ne suka samar da hotunan baki daya.