Nigeria: Shugaba Buhari ya gana da 'yan matan Chibok

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari da 'yan matan Chibok

Asalin hoton, Nigeria Government

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin 'yan matan sun haihu bayan da aka yi musu auren dole

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari, ya gana da 'yan matan Chibok 21 da mayakan Boko Haram suka sako, bayan shafe fiye da shekara biyu a hannunsu.

A ranar Alhamis ne aka sako 'yan matan sakamakon yarjejeniyar da aka cimma da mayakan, wacce kungiyar Red Cross da kasar Switzerland suka shiga tsakani.

Shugaba Buhari ya ce "Sun ga dukkan wani abu mai muni da dan adam zai iya gani a duniya. Yanzu lokaci ya yi da za su hadu da abin alheri".

Ya kara da cewa, gwamnati za ta kula da lafiyarsu, da inganta rayuwarsu sannan kuma ta tallafa musu.

"Gwamnatin tarayya za ta sauya rayuwarsu, sannan ta tabbata cewa sun koma sun ci gaba da rayuwa cikin al'umma ba tare da bata lokaci ba".

A watan Afrilun 2014 ne dai Boko Haram ta sace 'yan matan sama da 200, a makarantarsu da ke garin Chibok, na jihar Borno, a lokacin da suke jarrabawa, lamarin da ya ja hankalin duniya.

Kuma a ranar Lahadi ne suka gana da iyayensu cikin annashuwa, a karon farko tun bayan sace su.

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari da 'yan matan Chibok

Asalin hoton, Nigeria Government

Bayanan hoto,

A ranar Alhamis ne aka karbo 'yan matan daga hannun Boko Haram

Shugaba Buhari ya ce baya ga ceto su, gwamnati ce ke da alhakin kula da karatunsu da kuma taimaka musu cimma burinsu na rayuwa.

"Lokaci bai kure ba na su koma makaranta domin cigaba da karatunsu. Za mu kasance tare da su domin tallafa musu a kodayaushe," a cewar shugaban.

Shugaban ya kuma yi alkawarin yin duk abin da ya kamata domin ganin an ceto sauran 'yan matan da suka rage a hannun 'ya'yan kungiyar.

Sai dai rahotanni sun ce fiye da 100 daga cikin 'yan matan na Chibok 218, sun ce ba sa so su bar hannun kungiyar ta Boko Haram.

Bayanai sun nuna cewa an yi musayar yaran ne da wasu mayakan Boko Haram da gwamnati ke tsare da su.

Sai dai jami'an Najeriya sun ce ba wani daga cikin manyan mayakan kungiyar da suka yi musaya kafin sakin 'yan matan, haka kuma ba su biya kudin fansa ba.

Uba da 'yarsa

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Iyayensu sun ce ba su yi tsammnin za su sake ganawa su ba