An cimma matsaya kan dumamar duniya

Na'urar sanyaya daki na dauke da mugun sinadarin
Bayanan hoto,

Na'urar sanyaya daki na dauke da mugun sinadarin

Fiye da kasashe 150 sun amince da wata yarjejeniya domin kawar da sinadarin da ke taimakawa wajen kara dumamar da duniya ke yi.

Sinadarin Hydroflurocarbons (HFCs), wanda ake samu a cikin firinji da na'urar sanyaya daki da kuma sinadaran da ake fesawa irin su maganin kashe kwari ko sauro na fesawa, na yin matukar illa ga muhalli.

Wakilan kasashen da ke taro a Rwanda sun amince da wani garambawul da aka yi wa yarjejeniyar Montreal, wacce ta bukaci kasashe masu arziki su rage yawan sinadarin HFC zuwa shekarar 2019.

Sai dai masu suka sun ce wannan matakin ba zai yi tasiri sosai wajen rage dumamar da yanayi ke yi ba.

Sakataren wajen Amurka John Kerry, wanda ya jagoranci taron da ake yi a Rwanda, ya ce matakin babban ci gaba ne wajen samun lafiyar duniya.

Ya kara da cewa,"Wannan babban ci gaba ne domin kuwa zai taimakawa kasashe daban-daban wajen inganta muhalli saboda zai sa a rage dumamar yanayi da kimanin rabin digiri."