Hillary Clinton 'yar kwaya ce, in ji Trump

Donald Trump and Hillary Clinton

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Trump dai na kara rasa goyon baya a wasu muhimman jihohi.

Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump ya zargi abokiyar takararsa Hillary Clinton da shan wasu kwayoyi a lokacin muhawarar karshe da suka yi.

Ya ce ya lura da yadda kwayar ta hau kanta a farko muhawarar.

Mr. Trump ya bukaci a yi musu gwajin shan kwayoyi kafin su fafata a muhawararsu ta karshe da za a yi a ranar Laraba.

Sai dai ofishin yakin neman zaben Mrs. Clinton ya ce masu zabe za su iya gane cewa Trump na yin yunkuri ne kawai na yi wa zaben zagon-kasa.

Trump dai na kara rasa goyon baya a wasu muhimman jihohi.