Thailand ta jingine nadin sarki da shekara 1

Yarima Vajiralongkorn

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ba a dai san tsawon lokacin wannan rikon kwaryar dauka ba

Gwamnatin Thailand ta jingine nadin wanda zai gaji marigayi Bhumibol Adulyajed a zaman sarkin kasar bayan da yarima mai jiran gadon sarautar ya bukaci a jingine nadinsa har sai bayan akalla shekara daya.

Jami'an gwamnatin kasar sun ce har yanzu yariman Maha Vajira Longkorn bai shirya wa hawan gadon sarauta ba, abin da ke nufin wani wakilin sarki ne zai mulki kasar har ranar ya aka nada shi.

A yanzu dai an bayyana sunan Prem Tinsula Nonda wani aminin marigayi Sarki Bhumibol Adul yadej- mai shekaru 96- a zaman wakilin da zai rike masarautar a madadin Yarima Vajira Longkorn.

A cikin wani jawabi da yammacin ranar assabar, Farayin minista Prayuth Chan-Oca ya ce Yarima Maha Vajiralongkorn mai shekaru 64 ya bukaci 'yan kasar da su taimaki junansu a cikin wannan halin na bakin ciki da kasar ta shiga a maimakon damuwa da batun hawansa mulki.

Sarkin mai rikon-kwarya

Prem dai shi ne ke jagorantar majalisar mashawartan sarki na kut-da-kut ga Sarki Bhumibol kuma yana da kusaci ga 'yar sarkin da tafi shahara wato Gimbiya Maha Chakri.

A bisa kundin tsarin mulkin kasar dai shugaban wannan majalisar ta ne zai rike masarautar a zaman wakilin sarkin a cikin irin wannan halin.

Yanzu haka dai dubun dubatar mutane na ci gaba da kwarara zuwa fadar sarkin domin yin ban girma na karshe ga gawar basaraken wanda ake matukar kauna wanda kuma kusan duk wani dan kasar ta Thailand da ke da rai a yanzu ba sai kowane sarki ba face shi.

Hukumomi dai sun bar mutane su shiga fadar na wani dan takaitacce lokaci domin su sanya hannu kan kundin sunayen masu ta'aziyya.