An sace kayan agajin da aka kai Haiti

'Yan kasar ta Haiti sun kai wa masu bayar da agaji hari

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yan kasar ta Haiti sun kai wa masu bayar da agaji hari

Wasu 'yan kasar Haiti wadanda suka fusata sun sace kayan tallafin da motoci suka kai musu a daidai lokacin da Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya ke ziyara a kasar.

Mahaukaciyar guguwa mai dauke da ruwan sama ce dai ta afka wa kasar a watan jiya, lamarin da ya kai ga rasa rayukan akalla mutum 900.

Ban Ki-moon ya ce ya ga lokacin da mutanen ke satar kayan agajin a yankin Les Cayes, inda ya yi alkawarin kai karin kayan agaji ga 'yan kasar ta Haiti.

Ya bukaci kasashen duniya su kara kaimi wajen taimakon da suke bai wa Haiti.

Jami'ai sun ce akalla mutum 1.4 m ne ke bukatar tallafin gaggawa.

Ana fargabar cewa cutar amai da gudawa za ta barke a kasar, kuma tuni aka bayar da rahotannin mutuwar mutane da dama a kudu maso yammacin kasar.