'Yan matan Chibok sun gana da iyayensu

Uba da 'yarsa

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

'Ba mu taba tsammnin za mu sake ganawa da iyayenmu ba'

'Yan matan sakandaren Chibok 21 da mayakan Boko Haram suka sako ranar Alhamis, sun samu ganawa da iyayensu, bayan shafe fiye da shekara biyu ba sa tare da juna.

'Yan matan sun bayyana irin halin da suka samu kansu a lokacin da ake tsare da su, inda daya daga cikinsu ta ce ba ta taba tsammanin za ta kubuta daga hannun 'yan Boko Haram ba.

Wasu daga cikin 'yan matan sun bayyana yadda suka shafe kwanaki 40 babu abinci, amma duk da haka Allah ya tserar da su.

Haka kuma daya daga mahaifan 'yan matan ya ce yana fatan su ma sauran da har yanzu suke hannun 'yan Boko Haram din za a sako su.

Gwamnatin Najeriya ce ta hada iyayen da 'yan matan na Chibok a ranar Lahadin nan a Abuja babban birnin kasar.

Mai magana da yawun shugaban Nigeria kan harkokin watsa labarai Malam Garba Shehu, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, gwamnati na kokarin 'yanto sauran 'yan matan.

Mayakan Boko Haram dai sun sace 'yan matan sama da 200 a makarantarsu a garin Chibok, a lokacin da suke jarrabawa, lamarin da ya dauki hankalin duniya.

Kungiyar agaji ta Red Cross da gwamnatin kasar Switzerland ne suka shiga tsakani wajen ganin kungiyar ta Boko Haram ta sako 'yan matan, abin da kungiyar ta ce za ta yi idan gwamnatin Nigeria ta sako mata kwamandojinta.

Hukumomin Nigeria dai sun ce ba wani daga cikin manyan mayakan kungiyar da suka yi musaya kafin sakin 'yan matan, haka kuma sun ce ba wani kudin fansa da aka bayar don sakin nasu.