Ethiopia: An haramta kunna rediyo da talabijin

Fraiminista Hailemariam Desalegn
Bayanan hoto,

Gwamnatin Fraiminista Hailemariam Desalegn na fama da tarzomar 'yan hamayya

Gwamnatin Ethiopia Habasha ta bayyana sabbin dokoki na dokar ta-bacin da ta kafa a makon da ya gabata, sakamakon tarzomar da aka shafe watannni ana yi a kasar ta yankin gabashin Afrika.

An dai kashe daruruwan mutane a yayin tarzomar da manyan kabilun kasar biyu, wadanda ke cewa an mayar da su saniyar ware ta fannin siyasa da kuma tattalin arziki, suke yi a tsawon watannin tarzomar.

Daga cikin abubuwan da dokar ta haramta har da kama tashar rediyo da talabijin na 'yan hamayya, da yin duk wata mu'amulla da kungiyoyin da gwamnti ta ayyana a matsayin na 'yan ta'adda.

Jami'an diflomasiyya ma ba a barsu ba, domin daga yanzu ba a yarda duk wani jami'in diflomasiyya ya yi bulaguro zuwa wani wuri da ya wuce nisan kilomita 40 ba, daga babban birnin kasar, Addis Ababa.

An kuma haramta wa al'ummomin da ke yankunan kan iyakar kasar da kuma na inda manyan hanyoyin kasar suka ratsa, rike makamai da duk wani abu mai saurin kama wuta.

An kuma sanya dokar hana zuwa wasu masana'antu da gonaki da kuma wasu ma'aikatu da cibiyoyin gwamnati.