An dakile hari a gidan yarin Koutoukale

Jami'an tsaro a bakin aiki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jamhuriyar Nijar ta kan fuskanci hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram

Jami'an tsaro a jamhuriyar Niger, sun dakile wani harin da masu kishin Islama kusan su 100 suka kai gidan yarin KoutouKale da safiyar ranar Litinin.

Rahotanni dai sun ce da asuba ne maharan suka kai harin a gidan yarin mai tsananin tsaro, wanda ke da nisan kilo mita 50 daga Yamai, babban birnin kasar.

Wakilin BBC ya ce maharan mambobin wani bangare ne na kungiyar al-Qaeda mai suna Mujao.

Ministan cikin gida na kasar, Mohamed Bazoum ya tabbatar da mutuwar mutum daya daga cikin maharan.

Ya ce "zan iya tabbatar da cewa mutum daya daga cikin maharan, ya mutu. Yana sanye da rigar kunar-bakin-wake."

Wani dan jaridar kasar, ya ce maharan dai sun bullo ne daga iyakar kasar da Mali.

Masu tsaurin kishin Islama na kasar Mali dai sun kasance barazana ga jamhuriyar ta Niger.

Haka kuma, kasar na fama da hare-haren kungiyar Boko Haram, wadanda suke shiga cikinta daga makwabciyarta Najeriya.