Ya kamata Buhari ya duba kalaman matarsa — Okorocha

Okorocha ya kara da cewa saboda haka ya kamata a dubu korafinsu.

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Rochas Okorocha ya ce mutane suna bayyana rashin jin dadinsu da tafiyar gwamnatin APC

Gwamnan jihar Imo a Najeriya, Rochas Okorocha, ya bi sahun matar shugaban kasar, Aisha Buhari wadda ta yi korafin cewa mijinta ya yi watsi da 'yan jam'iyyarsa ta APC a harkokin mulki.

Rochas Okorocha ya ce ya kamata shugaba Buhari ya saurari korafin matar tasa musamman wajen yi wa mukarraban gwamnatinsa garanbawul.

Okorocha wanda ya bayyana hakan a karshen mako, ga 'yan jaridu, a fadar gwamnati, ya ce, "tabbas ni gwamna ne kuma na san inda gizo yake sakar."

Ya kara da cewa "idan dai har akwai kiraye-kirayen da ake yi wa shugaban kasa na ya yi wa mukarraban gwamnatinsa garanbawul, hakan ba zai zama laifi ba."

Aisha Buhari dai, a wata hira da ta yi da BBC, ta yi korafin cewa mijinta yana neman ya yar da kwauren ganga bayan gama cin moriyarta.

Aisha ta ce Buhari ya kawo wasu kalilan wadanda ba 'yan siyasa ba sun zagaye shi, a inda suke hana ruwa gudu.

Sharhi, Usman Minjibir, BBC Hausa, Abuja

Bayanan hoto,

Aisha Buhari ta ce ya kamata a sauya yadda al'amura ke tafiya a gwamnatin Shugaba Buhari

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

'Yan jam'iyyar APC dai wadda ita ce take mulkin kasar, suna ta faman korafi dangane da salon tafiyar gwamnatin Muhammdu Buhari.

Wasu na cewa shugaban bai yi abin da ya kamata ba wajen nade-nade a gwamnatinsa saboda kin cusa 'yan jam'iyyar da suka sha wahala a lokacin yakin neman zabe.

Wasu ma na yi wa wannan al'amari kallon wata matsala da za ta iya janyo jam'iyyar ta samu cikas ko kuma ma nan gaba ta dare.

Ko da mataimakin Sakatern watsa Labarai na jam'iyyar ta APC, Tim Frank, sai da ya gasgata batun da Aisha Buhari ta yi.

Mista Tim ya kuma ce daman sun dade suna hannunka-mai-sanda dangane da wannan matsala amma ba a saurare su ba.

Sai dai kuma wasu 'yan kasar na yi wa al'amarin kallon abin da ya kamata, a inda suka ganin hakan kamar ya nuna shugaba Buhari mutum ne mai zaman kansa.

Domin a cewarsu, cancanta ce gaba da kasancewa dan siyasa, a inda wasu kuma suke da ra'ayin cewa kamata ya yi tafiyar ta kunshi gogaggu da 'yan siyar gaba daya.