Sarkin Rwanda ya mutu

Jean-Baptiste Ndahindurwa ne sarkin karshe na Rwanda kafin a haramta sarauta a kasar
Bayanan hoto,

King Kigali V, ya yi gudun hijra a 1961 zuwa Amurka

Sarkin da ya rage na karshe a Rwanda, da aka fi sani da King Kigeli V, mai shekara 80, ya mutu, a Amurka.

King Kigeli V, wanda sunansa na asali, Jean-Baptiste Ndahindurwa, ya hau gadon sarauta a 1959 zuwa 1961, a lokacin da aka haramta sarauta a Rwanda.

A shekarar ne kuma aka tilasta masa yin gudun hijra, a inda ya samu mafaka a Amurka har ma ya kafa wata gidauniya ta taimakon marayu da 'yan gudun hijrar Rwanda.

Wata jaridar birnin Washington ta gano sarkin yana kan tsarin ciyar da marasa karfi abinci sannan kuma yana zaune a wani gida mai araha da Amurka ke biyan wani bangare na kudin hayar.

A ranar Lahadi ne dai aka sanar da rasuwar tasa a shafinsa na intanet.