An sanya dokar hana fita a Kaduna

Hakan ya sa an samu rasuwar mutane da dama
Bayanan hoto,

Jihar Kaduna dai ta sha fama da rikicin Makiyaya da Manoma

An sanya dokar hana fita ba dare ba rana, a karamar hukumar Jama'a da ke jihar Kadunan Najeriya.

Hakan dai ya biyo bayan tashin hankalin da ya janyo mutuwar mutane biyu ranar Lahadi, sakamakon wani hari da ake tsammanini Fulani makiyaya ne suka kai garin.

Sai dai kuma rahotanni na cewa mutanen da suka mutu sun kai guda 20.

A daren ranar Asabar ne dai aka kai harin, inda rahotanni ke cewa an kashe mutane da dama.

Tuni dai aka tsaurara matakan tsaro a yankin da ya dade yana fama da rikici.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Kaduna, ASP Aliyu Usman ya tabbatar da afkuwar hakan.