'Duk mai son yin Diploma ya tafi kwaleji'

Mallam Adamu Adamu
Bayanan hoto,

Ministan ilimi na Nigeria, Mallam Adamu Adamu

Hukumar da ke sa ido kan jami'oi ta Najeriya, NUC, ta haramta karatun diploma da jami'o'in kasar ke bayarwa.

Hukumar ta ce duk da cewa jami'o'in sun kwashe shekara da shekaru suna yin hakan a wurinta sun sabawa ka'ida kuma karatun haramtacce ne.

Guraben karatu da jami'oin gwamnatin kasar ke samarwa dai sun yi karanci ga miliyoyin mutanen da ke bukatar karatu mai zurfi a kasar duk kuwa da cewa an samu yawaitar jami'o'i masu zaman kansu fiye da a baya a kasar.

Daraktan hulda da jama'a na hukumar ta NUC, Mallam Ibrahim Usman Yakasai, ya gaya wa BBC cewa, in ban da diplomar da ake yi a jami'ar ABU, tun lokacin Frimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello, Sardauna, ba a yarda da duk ta wata jami'a ba.

Jami'in ya ce duk dalibin da yake son yin karatun diploma sai ya je kwalejojin kimiyya da fasaha (polytechnics), amma ba jami'a ba.