Za a tsagaita wuta a Yemen

Rikicin Yemen
Bayanan hoto,

Bangarorin biyu za su yi aiki da wata hukuma da za ta tabbatar da mutunta yarjejeniyar

Dukkan bangarori biyu da ke fada da juna a kasar Yemen, sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwana uku da za ta fara aiki a ranar Alhamis.

Majalisar Dinkin Duniya wadda ta shiga tsakani ta yi maraba da matakin, tana fatan hakan zai kawo karshen zubar da jinin da ake yi a kasar.

Tun da fari shugabannin gwamnatin Yemen da ke gudun hijira a Saudiyya, sun nuna alamun a shirye suke su dakatar da bude wuta, matukar 'yan tawayen Houthi da ke iko da babban birnin kasar Sanaa, sun amince da yarjejeniyar tare da janye kawanyar da suka yi wa birnin.

'Yan tawaye na Houthi, mabiya Shia da ke samun goyon bayn Iran, sun tilasta wa Shugaba Abdrabbuh Mansour Hadi tserewa daga kasar a shekarar 2014, ya yin da Saudiyya daga baya ta shiga jagoranci kawancen da ke kokarin fatattakar 'yan tawayen.